Shugabannin kasashen larabawa suna shirin tinkarar matslar zaman lafiya a gabas ta tsakiya da wasu batutwa da suka shafi yankin a fara taron kungiyar kasashen na shekara shekara da za'a yi bana a Libya.
Gobe Asabar ce aka sa ran fara taron na kwana biyu,amma ministocin kasashen wajen kungiyar sun yi taro jiya Alhamis a asirce,a Sirte,gari dake kan gaba. Babban magatakardar kungiyar Amr Musa, yace sun amince su tara dala milyan dari biyar domin taimakawa falasdinawa dake zaune a birnin Kudus,inda Isra’ila ta bada sanarwar zata fadada gine ginen ‘yan share wuri zauna.
Amr Moussa,yace babbar abindaya fi daukar hankalin taron shine hadin kan larabawa.Duk da wan nan furucin,tuni an sami tankiya a taron. Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshyar Zebari, ya dan fice daga zauren taron minsitocin,domin bayyana rashin jin dadin Iraqi,kan goyon bayan da shugaban Libya Moammar Gaddafi yake baiwa magoya bayan Saddam Hussein.