Faransa ta ce bai kamata shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kyaftin Moussa Dadis Camara,ya koma kasar ba, domin komarwar ta sa tana iya haddasa yakin basasa.
Har yanzu Kyaftin Camara yana wani asibitin kasar Morocco inda aka kai shi a ranar 4 ga watan Disamba bayan da wani mukarrabinsa ya harbe shi a kai.
A lokacin da yake magana yau talata a gaban 'yan majalisar dokokin kasarsa, ministan harkokin wajen Faransa, Bernard Kouchner, yace yana fata Kyaftin Camara zai ci gaba da zama a waje ba zai koma kasar Guinea ba.
A ranar litinin, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun dora ma Kyaftin Camara laifi kai tsaye na kisan gillar da aka yi cikin watan Satumba a Conakry, babban birnin kasar, inda aka kashe 'yan hamayya su fiye da dari da hamsin (150) masu yin zanga-zanga. Rahoton masu binciken ya bayyana wannan kisan gilla a zaman laifin cin zarafin bil Adama, ya kuma yi kira ga Babbar Kotun Bin Kadin manyan Laifuffuka ta Duniya da ta dauki mataki kan wannan lamarin.
Rabon da a ga shugaban na Guinea ko kuma a ji ta bakinsa, tun ranar da aka harbe shi.
Har yanzu ba a kama mutumin da ya harbe shi ba, watau leftana Aboubacar "Toumba" Diakite. A makon jiya, Diakite ya fadawa gidan rediyon Faransa cewa ya harbi Kyaftin Camara ne a saboda shugaban gwamnatin sojan yayi kokarin dora masa laifin kisan gillar na watan Satumba.