Gwamnatin mulkin soja ta kasar Guinea ta jingine ci gaba da tattaunawar neman sulhu da kungiyoyin hamayya a yayin da shugabanta yake kasar Morocco yana jinyar harbinsa da aka yi a kai.
Ministan dimokuradiyya da raya kasa, Kanar Moussa Keita, yace gwamnati zata janye daga tattaunawar da ake yi a kasar Burkina Faso har sai Kyaftin Mousa Dadis Camara ya murmure ya komo bakin aiki a kasar Guinea.
A cikin jawabin da yayi ta gidan telebijin na kasar, Kanar Keita ya tabbatarwa da al'ummar Guinea cewar ba wai gwamnatin ta watsar da tattaunawar yanki da aka shirya don warware rikicin siyasar kasar ba ne.
Wani shugaban hamayya ya zargi gwamnati da laifin janyewa daga tattaunawar domin tsawaita zamanta a kan mulki. Mamadou Bah Baadiko na jam'iyyar UFD yayi kiran da a ci gaba da wannan tattaunawa.
Kungiyoyin hamayya sun yi kira ga Kyaftin camara da sauran shugabannin soja da su sauka daga kan mulki. Kafin a harbi shugaban, gwamnatin mulkin soja ta ce tilas ne Kyaftin Camara ya kasance wani bangare na duk wata gwamnatin rikon wkaryar da za a kafa.