Kotun tafi-da-gidanka ta Kano, wadda hukumar tace fina-finan Hausa take amfani da ita wajen ladabtar da 'yan fim ko mawaka ko marubutan da ta ke ganin su na kalubalantar ikonta da na shugabanta Alhaji Abubakar Rabo, ta yanke hukumcin daurin watanni uku da tarar Naira dubu 300, da kuma wani hukumcin na daurin shekara guda ko biyan tarar Naira dubu 10 a kan shahararren Fardusa na fina-finan Hausa, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama.
Kotun dake karkashin mai shari'a Mukhtar Ahmed, ta ce ta samu Iyantama da laifin gudanar da kamfanin shirya fina-finai ba tare da iznin hukumar Abubakar Rabo ba, haka kuma ya fitar da fim din nan mai suna "Tsintsiya" ba tare da hukumar ta tace ta ba shi izni ba. Fim din "Tsintsiya" ya zamo fim din Hausa na farko da ya lashe gasar "Zuma Award" na kasa baki daya a fannin fina-finai masu nazartar rayuwar jama'a.
Shi dai Hamisu Lamido Iyantama, ya musanta dukkan wadannan zarge-zarge guda biyu.
Idan ba a manta ba, Iyantama ya taba yin takarar kujerar gwamnan Jihar Kano. Jim kadan a bayan da ya shiga takarar ne aka gurfanar da shi gaban kotu ana zarginsa da gudanar da kamfanin yin fina-finai ba tare da rajista ba.
Daga bisani kuma, an tuhume shi da shirya fim din "Tsintsiya" wanda aka tsara da nufin neman hada kan kabilu dabam-dabam na Nijeriya su yi zaman tare su daina tashin hankali da juna, ba tare da iznin hukumar tace fina-finan Jihar Kano ba.
A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, shugaban hukumar, Alhaji Abubakar Rabo, ya lashi takobin cewa duk wanda ya keta dokokin hukumarsu,"komai girmansa, duk (connections) dinsa, da duk iya maganarsa, duk fitinarsa, duk kirkinsa, matukar ba zai bi dokar mutanen Kano ba,...to wallahi sunansa cinnaka daidai da murjewa."
Shi dai Iyantama yayi nuni da cewa dokar tace fina-finai a Nijeriya ta haramta tace duk wani fim da wata kasa mai huldar jakadanci da Amurka ta shirya. An shirya fim din "Tsintsiya" ne da tallafin asusun wanzar da zaman lafiya na ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya.