Hukumomin kasar Chile Sun sa idanu sosai a kan wasu duwatsu biyu masu aman wuta da suka fara yin gurnani.
Hukumomi sun ja kunnen mazauna kauyukan dake kewaye da dutsen Llaima mai aman wuta, wanda ke da tazarar kilomita 700 a kudu da Santiago, babban birnin kasar. A ranar asabar, wannan dutse mai aman wuta, mai tudun mita dubu uku, ko kilomita uku, ya farka daga barcin wata da watanni, ya fara yin tumbudin toka da narkakken dutse.
Haka kuma kwararru sun yi gargadi game da motsin da dutse mai aman wuta na Chaiten dake kudu maso gabashin kasar ta Chile, ya fara yi. Masana kimiyya suka ce a cikin 'yan kwanakin nan sun ga alamun dake nuna cewa dutsen yana iya yin aman wuta nan ba da jimawa ba.
A karon farko cikin dubban shekaru, dutsen Chaiten yayi aman wuta a cikin watan Mayu. Hukumomin yankin Los Lagos na Chile sun kwashe mutane dubu hudu dake zaune a wani gari shi ma mai suna Chaiten a kusa da dutsen.