Sunanta dai Maryam A. Baba, amma akasari idan mutum bai ce Sangandale ko kuma Maryam Sangandale ba, to zai yi wuya ma'abuta son wakokin zamani na Hausa su gane wadda ake fada. Daga lokacin da aka haife ta a Tal'udu a Unguwar Mai Nagge cikin birnin Kano, har ya zuwa wannan lokacin, Maryam Sangandale ba ta taba zaton za ta irin nasarar da ta samu a fagen wakoki ba.
Maryam A. Baba ta samo sunan Sangandale daga wata wakar da suka yi mai wannan suna tare da Misbahu M. Ahmed cikin fim din nan mai suna "Kansakali". Kamar yadda aka saba gani ga masu fina-finan Hausa da mawaka, irinsu Sa'adiyya Gyale (Sa'adiyya Mohammed) wannan sunan ya makale mata.
Kwanakin baya, Maryam Sangandale, wadda ita ma tana cikin kungiyar mawakan nan ta Sa'adu Zungur Entertainment Group, ta fito da faifanta na farko, wanda ba wakokin fim ba ne, mai suna "Hikima Taguwa" wanda a ciki ta rera wakoki irinsu "Rabo" "Samari" da makamantansu.
Wakarta mai suna "Rabo" ta janyo cacar-baki a saboda yadda wasu ke rade-radin cewa ta yi ne da wani babban jami'in gwamnatin Jihar Kano, har ma an hana saka wannan waka a gidan rediyon Jihar Kano. Ina gaskiyar wannan magana?
A cikin hirar da ta yi da filin "A Bari Ya Huce..." Maryam Sangandale ta tattauna kan wannan batu na wakar "Rabo" har ma da yadda ta faro waka da cikakken tarihin rayuwarta, da kuma yadda take harhada wakoki ko fito da karinsu.
Idan ana son jin wannan hira cikin filin A Bari Ya Huce sai a matsa rubutun dake saman wannan labarin.