Dan wasan kwallon kafar Atalanta ya mayarwa da manajansa, Gianpiero Gasperini, martani da cewar “akwai tsananin rashin mutuntawa” kalaman da yayi bayan ficewar kungiyar daga gasar zakarun turai a jiya Talata.
A sanarwar da ya fitar a yau Laraba a matsayin martani ga kalaman, lookman yace: “ba wai kawai ware ni da aka yi tayi bata min rai ba, tasa naji matukar rashin mutuntawa, saboda irin kwazo da jajircewar da nake yi a kullum domin taimakawa kungiyarmu ta samu nasara da kuma magoya bayan Bergamo masu ban mamaki.
“Tare da magoya bayanmu, ma a matsayinmu na kungiya mun ji matukar takaici da sakamakon na daren jiya. Yayin wasan, mutumin daya kamata ya doka fenaritin ne ya umarce ni in buga; kuma ni domin taimakawa kungiyar tamu na dauki gabaran yin hakan a wannan lokaci.
Lokacin da Gasperini ya sako dan wasan bayan an baiwa kungiyar tazarar kwallaye 5-1 a jumlar wasannin data buga da abokiyar karawarta amma cikin dakika 36 ta farke kwallo daya.
Sai dai, abin da ya janyo cece-kuce a wasan shi ne ana daf da tashi daga wasan Atalanta ta samu bugun fenariti kuma ta bayyana kamar Lookman ya kwace wa zabin farko da ake dashi na Charles de Ketelaere da Mateo Retegui damar dokawa.
Inda ya barar da damar, kuma Gasperini ya caccaki hakan bayan tashi daga wasan.
Dandalin Mu Tattauna