A Jamhuriyar Nijer an kammala karo na 45 na kokawar gargajiya ta bana a garin Dosso, inda Abba Ibrahim na Babban Birnin Yamai ya karbe takobin daga hannun Sarkin ‘yan kokowa Abdu Kadri mai lakanin Issaka Issaka na Dosso da ya lashe takobin a can baya har sau 6.
Abba Ibrahim ya yi wannan galabar ne gaban Farai ministan Jamhuriyar Nijar, da takwarorinsa na Mali da Burkina Faso, da jakadun kasashen ketare da dama da ke kasar ta Nijar, da ma kungiyoyin kasa da kasa, da gwamnonin kasar da sarakunan gargajiya.
Sai dai a cewar, Musa karshe shugaban club zabi sonka na Africa, kuma tsohon mataimakin shugaban kungiyar kokowar gargajiya ta jihar Tahoua, wannan karo doli su yi murna, saboda an dade ana cewa babu maza ‘yan kokowa a kasar.
An dai kamalla kokowar ta bana, inda zakaran Abba Ibrahim ya sha kyaututtuka da ruwan kudi, yayin da mutanen Dosso suka
koma gida cikin zullumin wannan kayen da zakaransu Issaka Issaka Abdu Kadri ya sha a garinsa.
Daga bisani Ministan wasanni da matasa na kasar, ya ce karo na badi kuma na 46 na wasa mafi farin jini a Nijar zai wakana ne a garin Tahoua.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Dandalin Mu Tattauna