WASHINGTON DC —
Shirin Tsaka Mai Wuya na wannan mako ya ci gaba da tattaunawa ne kan babban zaben Shugaban kasa a Ghana da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disamba, 2024, inda Hukumar Zaben Ghana ta ayyana tsohon Shugaban kasar John Mahama a mastsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa. Mr John Dramani Mahama ya lashe zaben da kashi 56.55 cikin dari na kuru'un da aka kada. Yayin da Bawumia na jam’iyyar NPP ya samu kashi 41.67 cikin dari.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna