Gwamnan Jihar, Nasir Idris ne ya bada umurnin ga al’ummar yankin da su kashe ta.
Aliyu Gado Magatakarda Babba na sarkin Yauri yace wannan Dorinar ta kashe wani hadimin sarkin Yauri, lokacin da ya je hakon kifi. Ya kara da cewa dorinar ta jirkice kwale-kwale da yake ciki ta danne shi sai da ya mutu.
Yankin Yawuri na jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya yanki ne da ke da ruwa, inda ake hada-hadar kasuwanci da ayukkan noma da sauran wasu ayukka cikin ruwa, hakan baya rasa nasaba da yadda manyan halittun ruwa suka gidandance a yankin.
Dorina dabba ce mai hadari wadda ake samu cikin ruwa kuma garin na Yawuri ya yi suna da wannan dabbar har ma ita ce alamar tambarin garin, sai dai kwanannan an samu wata Dorina da ke da sabuwar haihuwa ta zo boyon dan da ta haifa a wani gari dake cikin ruwa a Yauri.
Duk da yake akwai dokokin da suka tanadi a kare 'yancin dabbobi a Najeriya, a na ci gaba da fuskantar barazanar miyagun dabbobi da ke yin lahani ga bil adama a wasu sassa na kasar.
A saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna