Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Batun LGBTQ A Yarjejeniyar SAMOA - Abubakar Bagudu


Ministan Kasafi da Tsare Tsare, Abubakar Atiku Bagudu
Ministan Kasafi da Tsare Tsare, Abubakar Atiku Bagudu

Bayan ce-ce-ku-ce da muhawara da ƴan Najeriya ke tayi akan yarjejeniyar samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu, wanda ake zargin akwai amincewa da auren jinsi cikin daftarin yarjejeniyar da zaisa ƙasar ta samu lamunin daloli masu yawa, gwamnatin tarayya ta musanta wannan zargi.

A hirarsa da Muryar Amurka, Ministan Kasafi Da Tsare-Tsare, Abubakar Bagudu, ya musanta wannan zargi, kuma yayi karin haske kan wannan batu, inda yace dama yarjejeniyar tana nan shekaru da dama da suka gabata.

Yanzu kuma sabunta yarjejeniyar akayi, kuma babu batun auren jinsi, halasta luwadi da maɗigo.

Bagudu ya kara da cewa, yarjejeniyar samoa, ta haɓaka tattalin arzikin kasa-da-kasa ne, ta hanyar cinikayya da dai sauransu.

Babu Batun LGBTQ A Daftarin Yarjejeniyar SAMOA - Abubakar Bagudu
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG