WASHINGTON DC - Jirgin saman kamfanin Dana air mai lamba 5NBKI dauke da fasinjoji 83 ya kauce hanyarsa bayan daya sauka a bangaren tashi da saukar jirage na cikin gida na filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Legas.
Sanarwar da kamfanin jiragen saman ya fitar ta bayyana cewar babu fasinja da ya jikkata, kasancewar jami’an hukumar kwana-kwana sun isa wurin da al’amarin ya faru da wuri domin taimakawa wajen ceton fasinjojin, sannan fasinjojin sun sauka daga jirgin lafiya ba tare da wata matsala ba.
A cewar sanarwar, “kamfanin Dana Air na takaicin bayyanawa al’umma game da kaucewa hanya da daya daga cikin jiragenmu mai lamba 5NBKI yayi, wanda ya taso daga Abuja zuwa Legas a yau Talata 23 ga watan Afrilun da muke ciki.
“Muna farin cikin tabbatar da cewar dukkanin fasinjojin jirgin saman 83 da ma’aikatansa sun sauka lafiya ba tare da kwarzane ko fargaba ba sakamakon kwarewar da ma’aikatan namu suka nuna. Mun shaidawa Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama (NSIB) da takwararta ta NCAA Mai Kula da Sufurin Jiragen Saman Najeriya game da lamarin kuma injiniyoyinmu sun dakatar da jirgin daga tashi har sai an kammala bincike game da musabbabin hatsari.”
Dandalin Mu Tattauna