Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
A wannan shirin za a ji kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambaya kan tarihin Hausawan kasar Sudan da alakarsu da Hausawan Najeriya.
Babangida IBB Giyawa na Karamar Hukumar Goronyo, jahar Sokoto ne ya yi wannan tambayar.
Za kuma a ji amsar tambaya kan musabbabin yawan faduwar darajar naira da kuma jinkirin farfadowarta idan ta fadi.
Garba Nahali Kamba, jahar Kebbi, Najeriya ne ya yi wannan tambayar.
Malam Ibrahim Musa Audu na Kwalejin Horas da Malamai ta Tarayya (FCE) da ke Yola, Adamawa, Najeriya ya karasa amsar tambaya kan Hausawan Sudan.
Dr Ahmed Tukur Umar na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa Najeriya, ba bada amsar tambaya kan yawan faduwar darajar Naira.
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna