Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Me Ya Sa 'Yan Afurka Da Ke Waje Ba Su Son Komawa Don Taimaka Ma Kasashensu?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shiri na AmsoshinTambayoyinku.

TAMBAYA:

Kamar yadda yakan faru loto loto, yau za a ji tambayar ce daga bakin mai ita: "...Ranar 27 ga watan Oktoba da daddare na ji wata hira da Malam (Murtala Faruk) Sanyinna ya yi da wani mai fashin baki da ke Amurka mai suna Alhaji Garba Suleiman, wanda ya yi fashin baki a kan Kwamitin nan na mutum 12 da Shugaban Amurka, Joe Biden, ya nada - a cikinsa har da mutum biyu daga Najeriya don nemo hanyoyin ciyar da Afurka baki daya. Ina da tambaya uku kan wannan fashi baki da Malam Garba Suleiman ya yi:

1. Tambaya ta farko: Me ya sa 'yan Afurka da ke zauna a wasu kasashen duniya - kamar su Amurka, China, Ingila, Faransa Jamus - me ya sa ba za su dawo su taimaka ma kasashensu na Afurka ba?

2. Tambaya ta ta biyu: Mene ne tunaninsu game da rashin dawowa kasashensu?

3. Tambaya ta uku: Ko ba za su dawo ba, me ya sa ba za su turo shawarwari ma Najeriya da sauran gwamnatocin kasashen Afurka ba game da yadda za a inganta rayuwa da tattalin arziki ba - dayake sun zama tamkar gogaggu?"

MAI TAMBAYA: Kabiru Shayibu Usman Gwammaja, Kano.

AMSA: To idan mai tambayar, Malam Kabiru Shayibu Usman Gwammaja Kano, da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga kashi na farko na amsar da mu ka samo daga shi kansa, wanda aka yi hirar da ta janyo tambayar da shi, wato Alhaji Garba Suleiman (Madakin Saminaka).

A sha bayani lafiya:

10-21-2023 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU - Edited.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG