DAGA OFISHIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYAR NAJERIYA, SASHIN YADA LABARAI DA HULDA DA JAMA’A
Yuni 19, 2023
SANARWA
SHUGABA TINUBU YA YI RITAYA GA DUKKAN MANYAN HAFSOSHIN SOJIN KASAR, MASU BAYAR DA SHAWARA, DA KWANTAROLA JANAR NA KWASTAN, SANNAN YA NADA SABBI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya amince da ritayar dukkan hafsoshin sojin kasar da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Masu Bayar da Shawara, Kwantarola Janar na Kwastam da kuma maye gurabansu nan take.
Sabbin Jami’an Da Aka Nada:
S/N SUNA NADE NADE
1 Mallam Nuhu Ribadu Mai Bayar da Shawara Kan Tsaron Kasa
2 Manjo Janar . C.G Musa Babban Hafsan Tsaro
3 Manjo T. A Lagbaja Babban Hafsan Sojin Kasa
4 Rear Admirral E. A Ogalla Babban Hafsan Sojojin Ruwa
5 AVM H.B Abubakar Babban Hafsan Sojojin Sama
6 DIG Kayode Egbetokun Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda
7 Manjo Janar. EPA Undiandeye Babban Hafsan Chief of Defense Intelligence
Shugaban kasa ya kuma amince da wadannan nade naden:
S/N SUNA NADE NADE
1 Kanar. Adebisi Onasanya Kwamandan Dagarawan Tsaro
2 Laftana Kanar Moshood Yusuf Kwamanda 7 Guards Bataliya, Asokoro, Abuja
3 Laftana Kanar Auwalu B Inuwa 177, Guards Bataliya, Keffi, Jihar Nasarawa
4 Laftana Kanar M.J. Abdulkarim 102 Guards Bataliya, Suleja, Jihar Niger
5 Laftana Kanar Olumide A. Akingbesote 176 Guards Bataliya, Gwagwalada, Abuja
Haka zalika, Shugaban Kasar ya amince da nade naden wasu jami’an soji a Fadar Shugaban kasa ta kamar haka:
S/N SUNA NADE NADE
1 Maj. Isa F. Audu (N/14695) Babban Kwamandan Atilaren Gidan Gwamnati
2 Capt. Kazeem O. Sunmonu (N/16183) Kwamanda Na Biyu Na Atilaren Gidan Gwamnati.
3 Maj. Kamaru K. Hamzat (N/14656) Babban Kwamandan Sashin Bayanan Sirri Na Gidan Gwamnati.
Sanarwar ta nuna akwai sauran nade nade da dama na wadannan manyan jami’an soji da Shugaba Tinubu ya yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A lura cewa nadin na manyan hafsoshin soji, da Sufeto-janar na ‘Yan Sanda, da Kwantarola Janar na Kwastam sai an tabbatar kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya tanaba.”
Sa hannu:
Willie Bassey
Daraktan Labarai
A madadin: Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya.