Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Davido: Karo Na Farko Da Ya Fito Bainar Jama’a Bayan Rasuwar Dansa


Davido, hagu da tawagarsa a wajen bikin rantsar da kawunsa Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar Osun. (Twitter: Israel)
Davido, hagu da tawagarsa a wajen bikin rantsar da kawunsa Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar Osun. (Twitter: Israel)

Fitaccen mawakin Afrobeats a Najeriya, Davido ya bayyana a bainar jama’a a karon farko tun bayan rasuwar dansa.

A farkon watan Nuwamba dansa, Ifeanyi Adeleke mai shekaru uku ya rasa ransa bayan da ya fada cikin tafkin ninkaya a gidansu da ke Legas.

Davido da mahaifiyar Ifeanyi Chioma sun shiga yanayi na matukar alhini kamar yadda rahotanni suka nuna duba da cewa shi ne da tak da suke da shi a tsakaninsu.

Mawakin ya bayyana ne a bikin rantsar da kawunsa Ademola Adeleke a matsayin sabon gwamnar jihar Osun da ke kudancin Najeriya a ranar Lahadi.

Daya daga cikin hadinmansa da ake kira Israel ne ya wallafa hotunan Davido tare da tawagarsa a wajen bikin.

Da ma da shi aka yi gangamin yakin neman zaben kawun nasa wanda ya yi takara karkashin jam’iyyar PDP gabanin zaben da aka yi a watan Yuli.

Ademola Adelek ya doke gwamna mai ci Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG