Washington, DC - A wata hira da Abdulrahaman Kabir Jani na gidan rediyon jihar Katsina, dattijo Malam Ahmed Lema ya bada dan takaitaccen tarihin garin.
Ahmed ya ce Kwami gari ne na Fulani mai tazarar kilomita daya arewa da garin Batagarawa, a yau garin ya kunshi yankin Rogo, Tsauni, Gama, da kwalejin koyon aikin malunta da kuma kwalejin kimiya ta Hassan Usman da ke Katsina.
Kwamawa dai sun yi mu’amala da Hambalawa, ‘Yandakawa, da mutanen Agama. Hambalawa sune mutanen unguwar alkali a cikin birnin Katsina yanzu.
Wannan gari dai ya shahara wajen sana’ar noma, kiwo da ilimin addini kafin zuwan na boko. Wasu daga cikin abubuwan tarihi a garin sune itatuwan giginya, aduwa, da durumi.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.