A gidan man AP dake kan hanyar Maitama zuwa Hilton, inda motoci suka yi layi don shan mai, kwanaki biyu da suka gabata an samu rudanı tsakanın masu sayan maı da ma`aıkatan gıdan man bayan an gano cewar gurbataccen aka yi ta sayarwa mutane, Alıyu Mohammad daya ne daga cıkın wandan da wannan tsautsayı ya fada kansu kuma ya bayyana mana yanda lamarin ta shafe shi.
Shima Khalid Ismail wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya yi kari da cewa, yana cikin layin shan tun kafin sallar asuba amma har bayan sallar asubayin bai samu mai ba kuma aka ce mai ya kare. Jim kadan wadanda aka sayar musu da mai a baya sun dawo cewa akwai ruwa a ciki kuma da shugabannin gidan suka gwada tabbas ruwa ya gurbata man.
Na yi kokarin jin ta bakin shugabanin gidan man amma abin ya ci tura, kasancewar sun ce sun riga sun dauki mataki akai na biyan mutanen da tuni gurbataccen mna ya lalata musu motocinsu, toh sai dai kwararre a harkan man fetur da gas a Najeriya Muhammad Saleh Hassan ya yi mana Karin haske akan lamarin.
Hakazalıka na zanta da mataımakın shugaban kungıyar `yan kasuwan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta IPMAN, Alh. Abubakar Maıgandı kan yadda suke kallon lamarın.
Har yanzu dai ana fama da karancin man fetur a Najeriya lamarin da ta kara wahalhalun da yan’kasar ke ciki, kuma Idan za’a iya tunawa Kamfanin NNPC ta bakin shugaba Mele kyari ya yi gargadi kan hukunta duk wani dan kasuwa ko gidan mai da aka kama da laifin sayar da gurbataccen mai ga mutane ko siyarwa yan bunburutu da mai a fadin kasar.
Ga Shamsiyya Hamza Ibrahim da karin bayani daga Abuja: