A shirin A Bari Ya Huce na wannan makon mun karrama marigayi Gremah Boucar, shugaban gidan Radio da Talabijin na Amfani a Jamhuriyar Nijar, daya daga cikin tashohi masu zaman kansu na farko da suka kulla yajejeniyar aiki da Muryar Amurka.
Saurari cikakken shirin ka ji tarihin marigayi Grema Boucar da kuma yadda ya bunkasa aikin jarida a Jamhuriyar Nijar:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.