Hukumar Kula da Kafofin Yada labarai NBC a Najeriya, ta tuhumi tashoshin Telebijin uku masu zaman Kansu akan zargin taka rawa wajen fadada tashe-tashen hankula a Kasar, biyo bayan zanga zangar ENDSARS. Tashoshin sun hada da Channels, da AIT, da Arise. Sannan hukamr ta sanya masu takunkumi tare da biyan tarar Naira miliyan 2 zuwa 3.
Wakiliyar Sashin Hausa Medina Dauda ta tattauna da Babban Darektan Hukumar Forfesa Armstrong Edachaba inda ya yi Karin bayani cewa, hukumar ta ci tarar wadannan gidajen talabijin din saboda laifin kin bin ka'idojin yada labarai na kasa.
Sakataren Kungiyar ‘Yan Jaridu ta kasa Shuaibu Leman ya ce, yin irin wannan hukunci ba daidai ba ne, ya kara da cewa, su suna kallon matakin a wani yunkuri ne na musguna wa tashoshin talabijin da ‘yancin yada labarai.
Facebook Forum