Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta kasar Ingila ta sallami mai horas da 'yan wasanta Unai Emery, bayan watanni sha takwas da kama aiki.
Hukumomin kungiyar ta Arsenal sun ce sallamar sa na da nasaba da rashin tabuka abun kirki a kakar wasan bana, kama daga firimiya lig na kasar Ingila har zuwa cin kofin Europe na Turai a bana.
A ranar Alhamis da ta gabata ne kungiyar Eintracht Frankfurt, ta bita har gida ta doke ta daci 2-1 a matakin wasan rukuni zagaye na biyar.
A gasar Firimiya kuwa tana matsayi na 8 ne a tebur da maki 18, a ranar Lahadi zata ziyarci Norwich City a wasan mako na sha hudu.
Arsenal tayi wasanni bakwai ba tare da tayi nasaraba, kuma wannan ne munmunar yanayin da ta taba samun kanta tun daga shekarar 1992, kimanin shekaru 27, da suka wuce lokacin da ta buga wasanni takwas ba tare da tayi nasara ba a karkashin jagorancin George Graham.
Tuni dai Arsenal ta bayyana sunan mataimakin kocin Unai Emery kuma tsohon dan wasan tsakiyar ta Freddie Ljungberg, a matsayin wanda zai rike kungiyar na wucin gadi kafun a nada sabon koci.
Facebook Forum