Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ko Kamfanin Kasar China Na Leken Asirin Kasashen Duniya?


Ya duniya zata zama idan akace duk al’amurran, da mutane kanyi ana kallon su ta na’urar kyamara, da gwamnatin kasar China ta hada? Wani hamshakin kamfanin kasar China, da ke kirkirrar kyamara da akanyi amfani da su wajen tsaro, yana kara bunkasa.

Hakan na kara sa wasu mutane a fadin duniya cikin damuwa. Kamfanin “Hangzhou Hikvision Digital Technology” wanda gwamnatin kasar ke rike da ragamar shugabancin kamfanin. Kasancewar kasar China, itace kasa da tafi samar da na’urar kyamara mai yawa a fadin duniya.

Mafi akasarin kyamarorin nan suna dauke da manhajojin, da kan iya kama yanar gizo kai tsaye, wanda yanzu haka wadannan kyamarorin ana amfani da su a kimanin sama da kasashe dari 100, a fadin duniya.

Wadannan kyamarorin na dauke da karfin daukar hoto mai inganci, a kowane irin yanayi a rayuwa. Kamfanin dai sun bayyanar da wasu sabuwar kimiyyar su, da suke dauke da wata kyamara, da zata iya bayyanar da irin yanayin da mutun yake a yayin tukin mota.

Idan mutun yana tuki, kuma yana aikawa da sakon gaggawa a lokacin tuki, kyamarar zata bayyanar da hakan. Haka sabuwar kyamarar zamanin, tana iya bayyanar da wanene ke tukin mota, daga daukar kalan gashin matukin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG