Babu wata tabbatacciyar lamba, amma masana sun tabbatar da cewar babu wata kasa a duniya da ta mamaye, yankin kudancin kasashen Afrika, kamar kasar China. Kasar China, tayi shigo shigo ba zurfi ga kasashen kusa da hamada.
A wani rahoton da wata kungiya mai zaman kanta ‘Greenpeace’ ta fitar, a shekarar 2015, kimanin shekaru biyu kamin shekarar rahoton, kasar China na da tamfatsa-tamfatsan jiragen kamun kifi 426, a cikin teku dake yankin kasashen Afrika ta yamma.
A tsakanin shekarun 2000 zuwa 2011, kimanin kashi 64% na kudaden shiga da kasar ke samu a bangaren kamun kifi, suna fitowa ne daga wannan yankin na Afrika maso yamma. Wanda aka kiyasta kudin su zasu kai kimanin dallar Amurka billiyan bakwai $7B, kwatankwacin naira tirilliyan ashirin da daya. A cewar kungiyar ‘The Pew Charitable Trust’
Kamun kifi baya cikin hanyoyin samun kudin shiga ga kasar China, wanda yake kasa da kashi daya na karfin kudin kasar. Amma da yawa a kasar wannan itace sana’ar su, kuma hanyar rayuwa. A cewar Mr. Haibing Ma, shugaban tsangayar sa’ido ta duniya a kasar China.
Masu sana’ar kamun kifi ‘yan kasar China, sukan tafi kasashen Afrika wajen kamun kifi, domin kuwa kifaye a yankin kasar China, sunyi karanci matuka. Yawaitar kamun kifi a kasar China, ya jefa yanayin kamun kifi a kasar cikin halin ha’ula’i.
Facebook Forum