Sunderland ta sha kashi a gidanta daci 4-1 a hannun Arsenal
Manchester United tayi canjaras 0-0 da Burnley
Tottenham ta yi kunnen doki 1-1 da Leicester City
Westbromwich 0-4 Manchester City
Wartfotd tasamu nasara akan Hull City da kwallo 1-0
Middlesbrough 2-0 AFC Bournemouth
Crystal Palace bata ji da dadi ba a gidanta da ci 4-2 a hannun Liverpool
Everton 2-0 Westham
Southampton ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 2-0
A yau kuma za'a fafata tsakanin Stoke City da Swansea city
Da misalin karfe Tara na dare agogon Najeriya Nijar da kuma kamaru
A saman teburin firimiya kuwa Man City na mataki na daya da maki 23 da kwallaye 15
Arsenal na mataki na biyu da maki 23 da kwallaye 13
Liverpool na mataki na uku itama da maki 23 da kwallaye 11
A kasan teburin kuwa Hull City na mataki na sha takwas da maki 7
Swansea city na mataki na goma sha Tara da maki 5
Itakuwa Sunderland na kasan tebur ne a mataki na ashirin da maki 2 kacal.
-
Bala Branco
Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.
-
Ibrahim Jarmai
Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.