Newcastle United ta lallasa Preston da ci 6-0
Liverpool ta samu nasara a kan Tottenham da kwallaye 2-1
Arsenal ta sha Reading 2-0
Bristol ta sha kashi a gidanta da ci 2-1 a hannun Hull City
Ita kuwa Leeds United ta samu nasara a kan Norwich da ci 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi 2-2
A yau kuma za'a fafata a gasar cin kofin kalubale inda Kungiyar kwallon kafa ta Man United zata karbi bakuncin Man City
Southampton kuwa zata kara ne da Sunderland
Westham kuma da Chelsea.
Za'a yi wasanne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Nigeria Nijar da kuma kamaru.
-
Bala Branco
Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.
-
Ibrahim Jarmai
Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.