Bayanan tsaro a Najeriya na cewar jami'an tsaro dake jihar Kwara tsakanin kasar da kasar Benin suka cafke Hajiya Jamila Tangaza akan hanyarta ta ficewa daga kasar.
Da ma Jamila Tangaza na beli ne bayan da aka zargeta da yin ba daidai ba a ma'aikatar da tayiwa shugabanci a karkashin ministan Abuja. An nemi wanda ya yi mata beli ya kawota ba tare da samun nasara ba lamarin da yasa aka shiga nemanta ruwa a jallo.
Shugaban hukumar EFCC yace su ma sun samu bayanin cewa hukumomin tsaro sun cafketa yayinda tayi yunkurin arcewa daga Najeriya bayan da aka kama tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja wato Bala Muhammad tare da wasu manyan jami'an birnin..
An zargesu da bada kwangila ba bisa kaida ba. Haka ma sun fitar da wasu kudin bogi da suka karkatasu. Sun kuma sayar da filaye duk ba bisa ka'aida ba.
Shugaban hukumar EFCC yace aikin banza ne ta gudu daga kasar domin babu inda zata. Kasar ta rubutawa kasashen duniya kuma koina aka ganta za'a kamata inji Malam Magu shugaban EFCC.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani