Mataimakin wakili na musamman na sakataren Majalisar Dinkin Duniya game da Laberiya, yace shirin wanzar da zaman lafiyar a Laberiya yayi amfani sosai wajen samar da tsaro a kasar, bayan tashin hankalin da aka dade ana fama da shi a kasar dake yammacin Afirka. Yace yanzu lokaci ne da Labariya zata kula da harkar tsaron ta da kanta.
Cikin shekara ta 2003, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya samar da shirin da zai kare fararen hula da kuma taimakawa mutane da gwamnatin Laberiya, wajen samar da zaman lafiya a kasar.
Shi dai wannan shiri an zo karshensa ne ran 30 ga watan Yunin wannan shekarar, inda shirin zai maidawa Laberiya harkokin tsaron kanta.
Wakilin na musamman Waldemar Vrey yace, duk da yake wannan shiri yazo karshe, amma zai kasance a Laberiya don taimakawa gwamnatin kasar.
Haka kuma Vrey, ya yabawa sauran kasashen da suka taimakawa shirin, ciki harda kungiyar ci gaban
tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, da kuma Amurka.