Ganin cewa Man fetur ya fara samuwa a Najeriya, wasu masu ababen hawa suna kokawa da irin wahalar da suke sha kafi su samu siyan Man fetur a gidajen mai.
Salihu Mamman Hussaini, yace tafi masa sauki ya sha mai a kasuwar bayan fagge, domin Gwamnati ta dade tana cewa za’a samu sai dai an samu za’a gani.
Suma masu dakon albarkatun man daga kudu zuwa arewacin Najeriya, sun ce suna tsaka mai wuya a halin yanzu inji Alhaji Sani Sambo, shugaban kungiyar masu dakon man a shiyar Kano.
Yace “yau duk wani mai Motar dakon mai abin tausayi ne duk Motar daukar mai a wata daya yakamata tayi sahu biyu zuwa uku a wata, tun da aka fara wahalar man nan ko da yaushe akwai Motoci zaune a inda ake dauko mai, yanzu akwai Motocin da suke wuce kwanaki arba’in zuwa wata biyu suna jiran mai.”
Ya kara da cewa duk wanda ya saye mota da kudin Banki a yanzu yana cikin mawuyacin hali.