A Nijar wasu hukumomi a kasar sun kaddamar da gangamin da zummar wayar da kan jama'a kan muhimmancin zaman lumana, sakamakon zanga zangar da ta kai ga kshe rayuka da lalata dukiyoyinmasu yawa da aka yi cikin kasar, sakamakon batuncin da ake zargin wata mujallar kasar Faransa ta yiwa addinin Islama.
Da yake bude taron a Maradi, Gwamnan yankin MAllam Abdu Mamman ya jaddada muhim,mancin zaman lafiya tareda ci gaba da rokon Allah ya tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umar kasar musulmi da kiristoci duka.
Shima da yake magana a taron Liman Tukur Abubakar yace shugaban kungiyar limaman ya shiga gidajen Radio inda yayi nasiha ga jama'a kan muhimmancin zaman lafiya.
Wakilan kungiyoyin farar hula suma sun halarci tarurruka.
Ga karin bayani.