A Saliyo hukumomin kasar sun haramta a gudanar bikin kirsimeti a bainar jama'a domin hana yaduwar cutar Ebola.
Wani kakakin gwamnati ya gayawa manema labarai jiya jumma'a cewa daga ranar 20 ga watan Disemba gwamnati ta haramta dukkan wani biki bainar jama'a, kwanaki biyar kamin ranar ta kirsimeti. Duk da haka dokar bata hana jama'a zuwa addu'o'in kirsimeti a a majami'u ba.
Kakakin gwamnatin Abdulai Bayraytay, yace an dauki matakin ne da niyyar hana jama'a masu yawa cudanya a bainar jama'a, domin hana cutar yaduwa.
Sai dai masu sukar lamirin gwamnati suka ce wannan mataki ba zai yi wani tasiri ba wajen shawo kan cutar, kuma zata yi katsalandan cikin 'yancin walwalar addini kamar yadda aka yi tanadi cikin tsarin mulkin kasar.
A makon nan ne hukumar kiwon lafiya ta duniya tace yanzu saliyo kasar da cutar tafi yin barna inda mutane fiyeda dubu takwas suka kamu da cutar, yayinda dubu daya da tari tara suka rigamu gidan gaskiya.