Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Nassarawa: ‘Yan Eggon Sun Ce Su Aka Fara Kashewa


Hoton da wani matafiyi mai suna Tijjani Mohammed ya dauka na inda matan 'yan sanda suka tare hanya a kusa da garin Lafia, Jihar Nassarawa.
Hoton da wani matafiyi mai suna Tijjani Mohammed ya dauka na inda matan 'yan sanda suka tare hanya a kusa da garin Lafia, Jihar Nassarawa.

Shugaban Kungiyar Raya Al’adun Kabilar Eggon, Chris Mamman, yace wasu manomansu biyu aka fara kashewa, daga baya kuma ‘yan kabilar Alago suka kama wasu Eggon biyu a Obi

‘Yan kabilar Eggon a Jihar Nassarawa ta Najeriya sun ce sune aka fara kai ma farmaki, aka kashe wani manominsu, sannan kuma aka kama biyu daga cikin ‘yan kabilarsu masu zuwa ta’aziyya a garin Obi, abinda ya haddasa rikici na baya-bayan nan ke nan da ya barke a tsakanin Eggon da Alago a Jihar Nassarawa.

Shugaban Kungiyar Raya Al’adun Eggon, Chris Mamman, yace wasu yara biyu ‘yan kabilar Eggon, daya mai shekara 17, dayan kuma mai shekara 9, sun tafi gona shuka wake ranar laraba, sai wasu mutane suka tare su suka far musu, inda suka kashe mai shekaru 17.

Yace daga baya wasu ‘yan kabilar Alago, sun tare hanya a garin Obi, suka far ma wasu ‘yan kabilar Eggon dake kan hanyar zuwa ta’aziyya, suka kama biyu suka mikawa soja. Su kuma ‘yan kabilar Eggon da suka fusata, sai suka yi magana da ‘yan kabilarsu a wasu garuruwan dake kan hanyar Obi zuwa Lafia, suka hana sojojin shigewa da wadannan mutane biyu.

Chris Mamman, yace sarkin Obi, wanda dan kabilar Alago ne, yayi musu alkawarin zai biya diyyar motar wadannan ‘yan Eggon da aka kona, kuma suka yarda suka bude hanya. Ya musanta cewa ‘yan kabilarsu sun kai farmaki suka kona gidaje da karkashe ‘yan kabilar Alago a Adabu da Obi.

Shugaban na Kungiyar Raya Al’adun Eggon, Chris Mamman, yace sun lallashi al’ummarsu kan su kwantar da hankulansu, amma ya roki hukumomi da su janyo hankalin ‘yan kabilar Alago a kan su daina kai farmaki kan ‘yan kabilar Eggon.

Ga cikakken bayaninsa na yadda abubuwan suka wakana a hirar da yayi da Ibrahim Alfa Ahmed
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG