Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ta Musanta Rubuce-rubecen Da Aka Ce Shugabanta Yayi


Hoton Kasar Najeriya
Hoton Kasar Najeriya

Babban bankin Najeriya ya musanta cewar gwamansa, Sanusi Lamido Sanusi, shi ne yayi wasu rubuce-rubuce kan albashin ‘yan majalisar dokoki ko kuma abubuwan da suke faruwa a kasar a kan wasu shafukan mu’amala na Internet, kamar facebook da Twitter.

WASHINGTON, D.C - Wata sanarwar babban bankin na Najeriya tace Malam Sanusi bashi da shafi ko guda daya a kan Facebook ko Twitter, kuma duk irin shafukan dake dauke da sunansa na karya ne da wasu mutane suka bude domin cutar jama’a ko kuma shafa masa kashin kaji.

Sanarwar ta ce a yanzu haka ma, hukumomi suna rike da wani wanda yayi amfani da irin wadannan shafukan bogi da sunan Sanusi Lamido Sanusi yana cutar jama’a, kuma kamfanin facebook ma ya rufe wasu shafukan fiye da 100 da aka samu suna amfani da sunan gwamnan ba tare da saninsa ba.

Idan ba’a manta ba, kwanakin baya wasu sun yi ta yada wani rubutun da aka ce wai shi Sanusi Lamido Sanusi ne ya rubuta inda a ciki ake zargin ‘yan majalisa da karbar kudaden alawus na fitar hankali.
XS
SM
MD
LG