Wakilin Sashen Samaliya na Muryar Amurka yace fashewar ta auku ne a wata rariya kusa da wani babban zauren taro na kasa, daidai lokacin da jami’an ma’aikatar leken asirin kasar Somaliya suke wucewa.
‘Yan sanda sun ce ana fakon jami’an ne da harin. A maimakon haka boma boman suka tarwatse kan wata karamar motar safa abinda ya yi sanadin kashe wadansu fasinjoji.
Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin harin da aka kai yau Litinin.
An fara samun zaman lafiya a babban birnin kasar Somaliya tun bayanda aka kakkabe kungiyar mayakan al-Shabab daga birnin a shekara ta dubu biyu da goma sha daya. Sai dai mayakan suna kai hare hare da kuma garkuwa da jama’a loto-loto.